Yau Talata shugaban addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya zargi abokan gabar Jamhuriyar ta Musulunci da laifin tayar da mummunar zanga-zangar kin jinin manufofin gwamnati da aka faro tun a makon da ya wuce.
Gidan talabijan na kasar Iran, ya ce an kashe wasu karin mutane tara cikin daren jiya, yayin zanga-zangar adawa da gwamnatin, wadda ya kara adadin wadanda suka mutu zuwa 20 sakamakon zanga-zangar da ta shafi tattalin arzikin kasar da aka fara kusan karshen makon da ya gabata.
A cewar rahoton, an kashe mutane shida a wani ofishin 'yan sanda a birnin Qahdarijan a wata arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga zangar da suka yi kokarin satar bindigogi.
Kafofin yada labarai na kasar sun ce an kashe wani dan sanda a Najafabad.
Shugaban Amurka Donald Trump, ya isar da sako a shafin sa na yanar gizo na Twitter, akan al'ummar Iran yau Talata inda ya ce, al'ummar Iran sun tashi tsaye domin kau da mulkin danniya a kasar.
Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani, ya lashi takobin cewa, jami'an tsaro za su maida martani akan 'yan zanga-zangar da kuma waddanda suka karya doka.
An kama daruruwan masu zanga-zangar tun lokacin da aka fara a ranar Alhamis a Mashhad, kafin zanga zangar ta yadu zuwa wasu sassan kasar.
Facebook Forum