Sabanin Sanarwar da Tayi Saudiya Ta Kai Hari Yemen.

'Yan Tawayen Houthi kasar Yemen

Saudiya ta lashe amanta saboda ta cigaba da kai hari Yemen.

Sojojin 'kawance da Saudi ke jagoranta sun kai sabbin hare-haren jiragen sama a Yemen a jiya Laraba, ‘yan sa’o’i bayan sanarwar tsagaita ruwan bama-baman da aka kwashe wata guda ana yi.

Hare-haren jiragen saman sun shafi sansanonin ‘yan tawayen Houthi a birnin Taiz da kuma gabar birnin Aden da ke kudancin kasar, a daidai lokacin da ake cigaba da fafatawa ta kasa tsakanin 'yan tawayen da magoya bayan shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi.

Bayan da ‘yan tawayen suka kwace sansanin daga hannun dakarun dake marawa shugaba Abd-Rabbu Hadi baya, an kai hari ta sama a wurin.

Ranar Talata Saudi Arabia ta fadi cewa ta kawo karshen hare-haren da ta kwashe wata daya tana kai wa da niyyar dakile dannawar da ‘yan Houthi ke yi, amma zata maida hankali akan neman masalaha a siyasance da ka iya hadawa da daukar matakan da zasu hana ‘yan tawayen na Houthi mallaka ko yin amfani da makaman sojojin Yemen.

A halin da ake ciki kuma, ‘yan tawayen na Houthi na kiran da a koma kan teburin shawarar da Majalisar Dinkin Duniya ke daukar nauyinsa don warware rikicin na Yemen.

A birnin New York mai magana da yawun Majalisar Stephane Dujarric yace, a shirye take wajen 'daukar kowane matsayi na ganin an samu sasantawa kan rigingimun na Yemen.