Sadiya Ibrahim Biu, Ma’aikaciyar jarida ce a gidan rediyo Progress da ke Jihar Gombe ta ce ta karanci harshen turanci a jami’a Bayero ta Kano duk kuwa da cewar ba abinda taso ta karanta Kenan ba a cewar ta. Amma ta tsinci kanta a aikin jarida kuma hakarta ta cimma ruwa.
Sadiya ta ce bayan ta kammala jami’a ne sai ta lura da cewa duk da ta karanci harshen turanci zata iya aikin jarida, amma tare da burin sake komawa karatu domin ta cimma burinta na karatun jarida.
Ta ce, ta so fannin jarida kasancewar mahifinta dan jarida ne, ta taso ta same shi yana aikin jarida hakanne ya sa ta yi sha’awar aikin jarida, ta kara da cewa ta fuskanci kalubale a yayi da take karatu domin ta yi karatu ne da aure sannan a farkon fara karatun ne ta rasa mahaifiyarta.
Sannan ta bayyana yadda tayi kokarin kammala karatu, duk da cewar ta dan samu kalubele saboda aure da karatu yana wahala, amma da taimakon mai gidan ta sai yazo mata da sauki.
Your browser doesn’t support HTML5