WASHINGTON D.C. —
Kwamandan mayakan Hutu na kasar Rwanda, wanda aka nema ruwa a jallo saboda zargin tafka laifukan yaki, an hallaka shi a Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
An kasha, Sylvester Muda-cumura, jagoran mayakan da ke kiran kansu Dakarun Dimokaradiyya Na Ceto Rwanda (FDLR a takaice), da safiyar jiya Laraba a lardin arewacin Kivu na Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo, a cewar majiyoyin soji da ke yankin, wadanda su ka yi magana da Shashin Afurka Ta Tsakiya Na Muryar Amurka.
Rundunar Sojojin kasar Congo ta tabbatar da mutuwar Muda-cumura din ta kafar twitter. Rundunar ta ce sojoji sun hallaka Muda-cumura a yankin Rutshuru, wanda ke daura da kan iyakar Uganda da Rwanda.