Ruwan Sama kamar da bakin kwarya, da aka dunga yi tun daga ranar Litinin din da ta gabata zuwa Talata a garin Ngandu dake jihar Borno, ya rugurguza gidaje fiye da 118, mazauna garin da yawa kuma suka rasa matsugunnan su.
Wasu daga cikin wadanda suka rasa gidajen su, da dukiya, sanadiyar ruwan saman da aka yi, sun bayyana yadda ruwan ya rusa gidanjen.
Hajiya Yaba Kolo, shugabar hukumar samar da agajin gaggawa a jihar Borno ta yi bayani akan agajin gaggawar da suka kai wa mutanen Ngandu. Tace sun kai kayan abince, barguna da zannuwan gado, da sauran wasu kayayyakin aiki a cikin gida.
Ya zuwa yanzu dai, ba wanda ya rasa rai sakamakon ruwan saman.
A saurari cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5