Ruwan Da Aka Sako Daga Kasar Kamaru Ya Hadasa Ambaliyar Ruwa A Adamawa Da Taraba

Bayan hukumomin kasar Kamaru sun yi gargadin cewa, a bana zasu sako ruwa da ga madatsar ruwan Ladgo, da ka iya shafan wasu jihohin Najeria uku, yanzu haka ambaliyar ruwa tuni ya soma barna a wasu sassan jihohin Adamawa da Taraba dake makwabtaka da Kamaru, wanda ya janyo samun asarar rayuka da dukiya.

A ziyarar jaje da ya kaiwa wasu da ambaliyar ta shafa, gwamnan jihar Adamawa Senata Muhammadu Bindo Jibrilla, ya gargadi jama’a dake zaune a gabar kogin Binuwai, da kuma masu gina gidaje a hanyar ruwa da ayi taka tsantsan don gudun irin abin da ya auku.

A baya dai dubban jama’a sun sha rasa muhallansu ta sanadiyar sako ruwa na Ladgo da jamhuriyar Kamaru ke yi, Kuma hakan na faruwa ne saoda kunnen kashi da gargadin da hukumomi ke yi na mutane su daina gini kan madatsar ruwa.

Saurari rahoton Ibrahim Abdul'aziz

Your browser doesn’t support HTML5

ruwan ladgo daga kasar kamaru ya hada ambaliyar rywa a adamawa da taraba 4'06