Daga 1 Ga Wata,Rasha Ta Tura Mai Ton Dubu 42 Zuwa China Ta Cikin Sabon Bututu

Shugabannin China da Rasha.

Jami’an China suka ce Rasha ta tura mata mai ton dubu 42 ta cikin sabon bututun mai da aka bude ranar daya ga watan Janairun bana.

Jami’an China suka ce Rasha ta tura mata mai ton dubu 42 ta cikin sabon bututun mai da aka bude ranar daya ga watan Janairun bana.

Ana sa ran Rasha zata tura mai ton milyan daya da dubu dari uku zuwa China zuwa karshen watan nan na Janairu.

Karkashin yarjejeniyar za’a yi jigilar mai ta sabon batutun ton milyan 15 duk shekara daga rijiyoyin mai a Rasha har zuwa shekara ta 2030.

Bututun man da ya samo asali daga garin Skovorodino can kuriya kasar, a yankin Amur dake gabashi, ya tsaya ne a birnin Daqing na china. Galibin bututun yana cikin China.

Bututun, wani reshe ne na bututu da ake kira East Siberia Pacific-Pipeline. Kowace kasa ta gina tsawon bututun dake cikin kasarta.

Wan nan bututu da ake kira East Siberia-Pacific, an gina shi da nufin jigilar mai daga Siberia galibi domin kasuwanni dake yankin Pacific.