Rundunar 'Yansandan Jihar Taraba Ta Gargadi 'Yan Siyasa Su Shiga Taitaiyinsu

PDP

'Yan bangan siyasa sun kai hari a garin Jalingo babban bairnin Taraba har ma wasu sun ji ciwo.

Ganin yadda 'yan bangan siyasa na 'yan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP ke cigaba da karawa da juna , rundunar 'yansandan jihar ta Taraba ta gargadesu su shiga taitayinsu.

Kakakin rundunar 'yansandan ASP Joseph Kwaji yace duk wanda aka kama da hannu cikin tada rikicin siyasa to zai dandana kudarsa. Yace su daina daukar doka a hannusu domin za'a hukuntasu kuma ko wanene. Suna magana da 'yan siyasa su ja kunnuwan magoya bayansu. Yace su zaman lafiya suke so.

Rundunar 'yansanda a shirye take ta dakile duk wata matsala da ka kunno kai. Yan sanda na kan bakarsu su tabbatar da zaman lafiya lokacin zabe da bayan zaben.

Alhaji Abubakar Bawa daraktan kemfen na Darius Ishaku wanda PDP ta tsayar yace basu ji dadin tashin hankalin da aka samu a Jalingo ba. Yace idan yaransu ne suka aikata fitinar zasu dauki matakin ladaftar dasu. Yakamata su gane cewa mai nasara baya fada kuma baya neman tsokana.

To saidai daya daga cikin 'yan takarar kujerar gwamna a PDP Chief David Sabo Kintiki yace basu amince da zaben Darius ba kuma suna nan daram akan bakarsu. Yace a saninsu ba'a yi zaben fidda gwani ba. Yace idan ba'a yi masu adalci ba zasu koma wata jam'iyyar.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar 'Yansandan Jihar Taraba Ta Gargadi 'Yan Siyasa Su Shiga Taitaiyinsu - 2' 34"