Kwamishanan 'yansandan jihar Mr. Sam Adegboye shi ya gabatar da wadanda ake zargin a gaban manema labarai a hedkwarsu dake cikin birnin Ibadan baban birnin jihar.
Kwamishanan yace sun sami nasarar kame muggan mutanen ne sanadiyar hadin kan wasu jami'an tsaro da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai tare da 'yan sintirin jihar. Kwamishanan ya bukaci jama'a da su cigaba da dinga ba 'yansandan hadin kai domin su zakulo masu aikata laifuka cikin jama'a.
Daya daga cikin wadanda aka cafke nan take ya amsa laifin da yayi. Wani kuma da ya sha da kyar yayi karin haske. Yace yana cikin motarsa matasa ukku suka kewayeshi da bindiga kana suka fitar dashi suka tasa keyarsa zuwa cikin wata motar suka kuma yi awan gaba da tashi.
Wata mata tace 'yan fashi da makami ne suka taresu suka fitar dasu daga motar kuma nan take suka harbe danta.
Ababen da aka samu daga hannun barayin sun hada da bindigogi da harsashai da motoci da kudaden jabu na gida da na waje.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5