Rundunar 'yansandan tace akwai shiri na musamman da 'yansanda suka bullo dashi domin yaki da wannan muguwar dabi'a.
Alhaji Abubakar Marafa kwamishanan 'yansandan jihar yace suna son Fulani su taimaki hukumomin 'yansanda da wasu na tsaro dangane da satan mutane da ake yi a jihar. Barayin sai su nemi a basu kudin fansa. Akwai kuma sace shanu wani zibin ma har da daukan rayuka.
Kwamishanan ya kira Fulani da su binciko mutane batagari dake aikata miyagun ayyukan. Yace mutanen suna tare dasu, sun sansu. Kamata yayi su tona asirin mutanen. Yace su yasu ne. Yace su koma kananan hukumominsu su zauna da babban jami'in 'yansandan wurinsu da Fulanin dake yankin su tace kansu.
Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah reshen jihar Neja Ardo Adamu Kaduna yace sun ji dadin taron domin yana da mahimmanci. Yace sun samu kungiyar matasansu da zata taimaka masu akan yawan sace-sacen da ake yi. Yace ana sace mutane da dabbobi. Zasu rantsar da matasan su shiga sako-sako kuma duk inda munafiki yake su zakuloshi. Matasan zasu hada hannu da jami'an 'yansanda.
Ardo Kaduna yace abun da ya damesu shine yadda ake sace yaro, a sace mace, a sace dattijo,kai hatta sarki ma ana saceshi. Babu wanda aka bari. Baicin hakan sai a kwashe dabbobi a shiga gidaje a kashe mutane.
Alhaji Useni Boso mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa wanda ya kasance a taron yace sun kira yara 'ya'yansu da su tashi tsaye su yaki wannan muguwar dabi'a. Yace zasu bada gudummawa akungiyance tare da yi masu duk abubuwan da suke bukata a yi.
Dangane da cewa sun san Fulanin dake aika aikar, Alhaji Boso yace wadanda suke jeji sun sansu amma suna tsoron za'a kai masu hari idan sun falalsasu. Ana kuma iya kashesu.
Daruruwan Fulanin da suka halarci taron sun goyi bayan a dauki tsauraran matakai akan matsalar satar mutane dake matukar ci masu tuwo a kwarya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5