An kamasu suna dauke da muggan makamai, da kayan da ake kyautatazaton na sata ne, da kudi naira dubu dari ukku da arba’in da uku da dari biyar.
Kwamishinan ‘yansanda Musa Kimo shi ya bayyana haka ga taron manema labarai a shelkwatarsa dake Yola inda ya nuna masu mutanen da ake tuhuma da kayayyakin da aka samu a hannunsu.
Muryar Amurka tayi fira da wasu daga cikin ‘yan fashin. Isyaku Ibrahim wanda ake kira Yellow da Hussaini Yahaya wanda aka fi sani da Dogo dukansu suka amince da aikata fashi da makami.
Malam Saidu Njidda wani matukin motar fasinja daga Yola zuwa Numan yace motocinsu basa binhanya da zara karfe biyar da rabi na yamma yayi, don a cewarsa a dai-dai wannan lokacin ne yan fashin ke fita su tare hanya suna kwace dukiyoyin jama’a , wani lokacin ma harda kisa.
Wannan kame da rundunar ‘yansanda ta jihar Adamawa tayi na zuwa ne makonni ukku da soma aiki na sabon kwamishinan ‘yan sandan a jihar da ta jima tana fama da matsalar ‘yan fashi da makami akan mayan titunan da suka hade jihar da jihohin dake makwaftaka da ita.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5