Rundunar Yan Sandan Zamfara Ta Cafke Yan Bindiga Barayin Shanu Su 17

Yan Bindiga Barayin Shanu A Zamfara

Yan Bindiga Barayin Shanu A Zamfara

Wannan shine karon farko a wannan shekara da rundunar ‘yan Sandan jihar Zamafara, ta sami gagarumar nasara, a yakin da take yi da ‘yan bindagar da ke kai hare hare a wasu yankunan jihar inda suke karkashe mutane tare da yin awon gaba da Shanunsu.

A wani sumame na musammam ne dai rundanar tace ya kai har da yin artabu da musayar wuta da Maharan, ta sami cafke wadansu mutane 17 da suka kunshi maza 15 da mata 2 wadanda ake zargin suna daga cikin yan bindigar.

Ko baya ga ‘yan Jarida da aka nunawa wandanda aka kama din gwamanan jihar Zamfara, ya ziyarci shedikwatar runduna yan Sandan jihar, inda kwamishinan yan Sanda yayi masa bayani akan kamen.

Gwamanan Zamfara Abdul’aziz Yaro Abubakar, wanda da alama yana zargin da akwai siyasa a tattare da hare-haren da yan bindagar ke kaiwa, yace wannan somin tabi ne kawai. Yaci gaba da cewa gwamnati zata ci gaba da daukar duk kwararen matakan da suka kamata don ganin an kawo karshen masu aikata duk irin wannan laifin.

Bayan makamai da aka samu ga wadanda ake zargin da suka hada da bindigogi kirar AK47 da na gargajiya dama Adduna da Gatura, haka kuma an sami Shanu 310 da Tumakai da Awakai 105 da Jakuna 22, da kuma Babura 12.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Yan Sandan Zamfara Ta Cafke Yan Bindiga Barayin Shanu Su 17 - 2'57