Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Biyu Na Mutuwa A Duk Kwanaki Uku Dalilin Cizon Macizai A Gombe


Zanen macizai kan bishiya.
Zanen macizai kan bishiya.

Bincike na nuni da cewar kimanin mutane biyu ne ke mutuwa a cikin kwanaki uku, a kauyukan Goldimare da kuma Iyadema a karamar hukumar Shongom dake jihar Gombe, a sanadiyar cizon macizai.

Garuruwan biyu wanda dubban mutane ke zaune a cikin su, suna kewaye ne cikin tsaunuka kuma babu hanya da kowanne irin abin hawa zai iya bi. A cewar Jonathan Jibril, wanda ke zama shugaban matasan garuruwan yace, suna fama da macizai ta ko ina saboda duk gonaki da ma kan duwatsu babu inda babu su. Kuma suna cizon mutane har a gidajen su.

Wani abin tada hankali shine yadda ake samun mace macen mata da yara wajen haihuwa, inda matan da suke mutuwa sukafi wanda suke haihuwa yawa. Hajiya Sa’adatu Mustapha Sa’ad Alkyabban Kaltingo, tace matsalar rashin hanyoyin da ake fama da su na daga cikin adilan da suka saka ake rasa rayukan wasu mata.

Bisa halin damuwa da mutanen yankin ke ciki kan wannan lamari yasa mai martaba Sarkin Kaltingo, Injiniya Sale Mohammed, hada gangami domin yin aikin gayya domin samar da hanya da akalla babur ko mota zasu iya bi domin dauko marasa lafiya a kaisu Asibiti cikin sauki.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG