Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ta Ce Za Ta Zage Damtse

.

Biyo bayan batun kyautata albashin ‘yan sanda da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umurni ayi, rundunar ta ce za ta zage damtse kan kiyaye rayukan jama'a da dukiyoyin al’umma.

Wakilin sashen hausa, Saleh Shehu Ashaka ya ziyarci helkwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya, inda ya zanta da mai ba babban sufeto shawara akan hulda da manema labarai, Bala Ibrahim gameda batun na kyautata albashi.

Yanzu dai za a jira a ga lokacin da wannan karin albashin zai fara aiki, daidai lokacin da sauran ma’aikata ke jiran tsammanin fara aiwatar da sabon mafi karancin albashin Naira dubu 30.

In za a tuna, wasu daga jami’an ‘yan sandan na kokawa kan yadda hatta alawus na aiki a yankuna masu hatsari da su ka shafi yaki da Boko Haram basa samu.

In dai karin albashi zai iya inganta rayuwar ‘yan sanda, za a jira a ga tasirin hakan ta hanyar daina ganin karbar na goro, da ake zargin yawancin jami’an na yi a kan tituna.

Your browser doesn’t support HTML5

Umarnin Shugaba Buhari Na Karin Albashin 'Yan Sanda 2'34"