Rundunar 'yan sandan jihar Neja tana binciken hukumar tsaro ta Civil Defense, NSCDC, akan mutuwar wani matashi Luka Makana da aka ce ya mutu ne a hannun hukumar a garin Bangi dake karamar hukumar Mariga.
Joseph Tanko mahaifin Luka ya ce jami'an tsaron farin kayan sun daure matashin ne suka dinga dukarsa har ya mutu. Civil Defense din dai ta zargi matashi ne da satar diyan mangwaro guda biyar. Ta bakinsa a cikin daji ne suka iske matashin inda suka kamashi suka kaishi ofishinsu. A nan suka daureshi suka dinga lakada mashi kashi.
Ya kara da cewa suna neman matashin ne sai suka ga 'yan sanda suna fitar da gawarsa daga ofishin Civil Defense. Dangane da ko sun tabbatar 'yan Civil Defense ne suka kasheshi, sai Joseph Tanko ya ce "daga ofishinsu aka fito da gawar matashin".
Shi ma kakakin 'yan sandan jihar ASP Abubakar Dan Inna ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma jami'an hukumar suna hannun 'yan sanda kana ana gudanar da bincike.
Amma kodayake jami'in yada labarai na hukumar NSCDC Malam Ibrahim Yahaya ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ciwon ciki ne ya kashe matashin. A cewarsa babu wanda ya taba shi.
Kawo yanzu wannan lamarin shi ne karo na uku da mutane suka mutu a hannun jami'an NSCDC a jihar ta Neja.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5