Ossy Ibory ya yi ‘kaurin suna wajen jagorantar fasa bututun mai tare da satar ‘danyan Mai a yankin Niger-Delta, da kuma fashi da makami a kan teku. Ossy ya yi ikirarin cewa yana da mayaka kimanin 7000.
Rundunar tsaro ta JTF ta sanar da bindige shararren ‘dan bindigar ne sakamakon musayar wuta da ta afku lokacin da suka kai wa ‘yan bindigar sumame. Wannan nasara da rundunar ta samu na nuna cewa da alamu za a samu saukin fashi da makami akan teku da sauran wasu birane dake yankin Niger-Delta.
Mai magana da yawun hedikwatar tsaron JTF dake yankin Niger-Delta, Manjo Abdullahi Abubakar, ya tabbatarwa da Muryar Amurka cewa dakarun sun kawo karshen Ossy Ibory, wanda yake shugaban masu tayar da kayar baya a yankin.
Matsalolin tsaro a yankin Niger-Delta ba wani sabon abu bane, kama daga barnar ‘yan bindiga masu fasa bututun Mai suna satar ‘danyan Mai da kuma masu satar mutane da garkuwa da su don neman kudin fansa.
Domin karin bayani ga rahotan Lamido Abubakar.
Your browser doesn’t support HTML5