Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karbi Wasu 'Yan Boko Haram Da Iyalansu

Rundunar Sojojin Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya tace wasu mayakan Boko Haram guda takwas da iyalansu goma sha hudu sunyi saranda ga dakarun Bataliya ta 152 a garin Baki dake karamar hukumar Bama a jihar Borno.

Jami'in sadarwa na aikace aikacen hedkwatar sojojin Najeriya Kanar Aminu Ilyasu yace a binciken farko da aka gudanar an gano wadannan da suka yi sarandar na daga cikin wadanda a baya suka yi ta kai hare hare tare da kisa, da ma satar mutane.

Mayakan sun yi nadamar danyen aikin da suka yi inda suka kara da cewa tun watanni hudu da suka gabata shugabancin kungiyar ta Boko Haram ta shiga rudani.

Suka ce yanzu haka akwai gungun mayakan da suke so su mika kai ga jami'an tsaro biyo bayan ruwan wuta da dakaru suke masu,.sannan ga mummunar baraka da ta bullo a tsakaninsu.

Bincike ya tabbatar da cewa daga watan jiya na Janairu zuwa yanzu kimanin kwamandoji 25 aka kashe a rikicin na cikin gida. Al'amarin da wasana tsaro ke ganin gwamnati na iya cin ribar rikicin.

A saurari rahoto cikin sauti daga Abuja a Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karbi Wasu 'Yan Boko Haram Da Iyalansu