Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Kai Wasu Hare-hare a Sambisa

Babban hafsan hafsoshin rundunar saman Najeriya Air marshall Sadique Abubakar

Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce jiragen yakinta sun kai wasu manyan hare-hare a yankin Bula Kurege da ke cikin dajin Sambisa.

Kakakin Rundunar Air Commodore Ibikunke Daramola, ya ce harin ya biyo bayan wani rahoton sirri da suka samu ne dake nuna cewa mayakan Boko Haram sun yi kaura zuwa wani yanki na dajin daga inda suke shirye-shiryen kai wani babban hari ga sojoji da fararen hula.

Jiragen yakin Najeriyar sun afka wa ‘yan ta'addan, duk da cewa wasu daga cikinsu sun yi yunkurin tserewa amma jiragen sun same su gab da lokacin.

Wannan sabon farmaki mai taken "Operation Decisive Edge" na zuwa ne biyo bayan kammala shirin operation “Rattle Snake 3”.

A cewar babban hafsan hafsoshin saman kasar, Air marshall Sadique Abubakar, an samu gagarumar nasara.

Ya ce “an kona kimanin sansanonin Boko Haram guda ashirin tare da kashe ‘yan ta'addan.”

Babban hafsan sojin saman ya kara da cewa sabon farmakin na da zumnar wargaza wuraren da ‘yan ta'addan suka bizne ababen fashewa dake dajin sambisa da ma tafkin chadin.

Saurari cikakken rahoto cikin sauti daga bakin wakilinmu Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kai Wasu Hare-hare a Sambisa