Bayan harin da ya hallaka mutane 30 a kauyen Bawar Daji da ke karamar hukumar Anka, jihar Zamfara. Babban Hafsan Sojin Sama, Sadique Abubakar ya bayar da umurnin tura dakaru na musamman zuwa Gusau, a wani yunkurin kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga da ake samu a jihar.
A wata sanarwa da suka saka a shafukansu na Facebook da Twitter mai dauke da sa hannun direktan yada labarai na Rundunar Sojan Saman Najeriya, Air Vice Marshall Olatokunbo Adesanya, dakarun da aka tura sun kware wajen yakin sama domin su tallafawa jami’an tsaron da ke kasa wajen kawar da hare-haren da ake kai wa mutanen da ba-su-ji ba ba-su-gani-ba. Sannan za a tura su zuwa lungu da sako na jihar.
Jihar Zamfara na ci gaba da fama da yawan kashe-kashen mutane duk da cewa an kashe Buharin Daji wanda ya yi kaurin suna wajen kai hare-hare da fashi da makami, da yin garkuwa da mutane. Na baya-bayannan da ya auku shi ne a kauyen Bawar Daji, inda ‘yan bindiga su ka yi diran mikiya suka hallaka mutane kusan 30.
Gungun ‘yan bindigar Buharin Daji ne suka dauki alhakin harin a matsayin ramuwar gayya bayan da aka kama yaransu da matansu.
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umurnin bindige duk wani da aka samu dauke da makamai ba bisa ka’ida ba, a yunkurin da take yi na dakile hare-haren 'yan bindiga.
Amma 'yan bindigar, wadanda aka sha zaman sulhu da su, sun ce wannan ba ita ce mafita ba.