Daraktan labarai na shalkwatar sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, ya yiwa wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Hassan Maina Kaina, Karin bayanin cewa rawar dajin da jami’am ke yi bayan kowace shekara domin tabbatar da kwarewar aiki, an kwashe kusan shekaru goma ba a yi ba,
Ta dalilin haka ne shugaban rundunar sojin kasar Janar Tukur Buratai, ya umurci jami’an su gudanar da wannan gwaji a dajin Sambisa, kuma za a yi gwajinne ta hanyar fafatawa Tsakanin rundunonin soji, domin inganta kwarewa wajan sanin makamar aiki da amfani da kanana da manyan makamai.
Da yake amsa tambayar da wakilin sashi Hausa, ya yi masa, Kuka sheka, ya bayyana cewa saboda matakan tsaro, da kuma yaki da ake da ‘yan kungiyar boko haram, baza su bari sai ta kwana ba duk da cewa an ci karfin kungiyar, ya kuma kara da cewa a yanzu haka akwai kimamin rundunoni bakwai dake jibge a wannan yanki da ke fama da rikicin boko haram.
Daga Abuja, ga rahoton Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5