Kwamandan mayakan Air Commodore Christopher Egoba ya ce sun bada kayan tallafin ne domin tallafawa rayuwarsu saboda sun tsinci kansu cikin maraici.
Dangane da mayakan Egoba yace ba aikin kare kasa kawai ba ne ya rataya akansu, har ma da na tallafawa al'umma. Dalili ke nan da suka yi anfani da ranar tunawa da shekaru 51 da kafa rundunar mayakan saman Najeriya su tallafawa marayu da nakasassu. Yace hakin kowane dan kasa ne ya tallafawa marayu da gajiyayyu.
Rundunar ta bada kayan abinci da suka hada da shinkafa da taliya da sabulun wanka da na wanki da man girki da dai kayan bukatu irin na yau da kullum.
Alhaji Aji Yusuf Gandu babban sakataren ma'aikatar mata ta jihar Borno shi ya karbi kayan a madadin marayun. Yace sun yi matukar godiya duk da matsalolin Boko Haram da mayakan ke fuskanta sun samu lokaci sun tanadi kayan da suka mika.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5