Rundunar Sojin Najeriya Ta Musanta Mutuwar Janar Lagbaja

Laftanar Janar Lagbaja

A ranar Asabar hukumomin sojin na Najeriya suka kore rahotanni da ke cewa an samu gibi a shugabancin rundunar sojin kasa suna masu cewa Janar Lagbaja ya tafi hutu ne.

Rundunar sojin Najeriya ta yi fatali da rade-radin da ake yi cewa Babban Hafsan Sojin Kasa Laftanar Janar Taoreed A. Lagbaja ya rasu.

A wani rubutu da ta yi da manyan haruffa akan wani labarin da aka wallafa a shafin X a ranar Lahadi, rundunar sojin ta Najeriya ta ce “Labarin na boge ne.”

Tushen labarin kamar yadda kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito daga Jackson Ude ne, wani tsohon hadimin shugaban kasa kuma mai sharhi a kafafen sada zumunta.

“Babban Hafsan Sojin Kasa, Taoreed Lagbaja ya mutu a wani asibiti a kasar waje tun kusan sa’ao’i 48 da suka wuce. Ya rasu ne sanadiyyar cutar daji da tsananinta ya kai mataki na uku.” Ude ya ce a shafin X.

Sai dai a sanarwar da rundunar sojin ta fitar a ranar Lahadi, ta ce batun babu gaskiya a ciki.

A ranar Asabar hukumomin sojin na Najeriya suka kore rahotanni da ke cewa an samu gibi a shugabancin rundunar sojin kasa suna masu cewa Janar Lagbaja ya tafi hutu ne.

Sai dai duk da musanta labarin da sojojin na Najeriya suka yi, Ude ya kara kalubalantar su.

“Idan rundunar sojin ta ce karya ne (abin da na fada), su fitar da bidiyon Janar Lagbaja na dakika daya a kwance akan gadon asibitinsa.” Ude ya ce a wani sabon sako da ya wallafa a shafin na X a ranar Lahadi.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina:

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojin Najeriya Ta Musanta Mutuwar Janar Lagbaja