Manjo Janar din yace rundunar sojin Najeriya na yin gargadi ga kowa da kowa musamman wadanda su keyin barazanar raba kasar.
Yace abun da su keyi tamkar cin amanar kasa ne da son sabbaba dukiya da rayukan jama'a.
Janar Ibet yace muddin aka gayyato sojoji su kwantar da yunkurin to ko zasu yi duk abubuwan da ya kamata cikin tsari da bin doka domin daidaita alamura.
Gargadin sojojin tamkar hannunka mai sanda suka yiwa 'yan rajin kafa kasar Biafra daga cikin tarayyar Najeriya..
Amma wani tsohon hafsan sojan saman Najeriya Aliko El-Rashid mai murabus yace a yi taka tsantsan. Idan an bi alamuran dake faruwa a duniya yakamata gwamnatin tarayya ta bi lamarin a hankali. Ba abu ba ne da za'a bi da karfin soja. Yayi misali da kasar Syria. Yace daga zanga-zanga da aka tura sojoji suna kashe mutane yanzu rikicin ya rikide ya zama na kasa da kasa.
Sale Jingir mai murabus wani tsohon sojan Najeriya yace yaki ba karamin abu ba ne. A yi hankali.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5