Makon jiya ne 'yan rajin kafa kasar Biafra suka gudanar da zanaga zanga wadda daka baya ta yi muni har suka soma maiwa 'yan arewa hari a birnin Fatakwal.
Nufinsu shi ne tursasawa gwamnatin Nageriya ta raba kasar su tafi da Biafra ta kuma sako wani daraktan rediyon Biafra mai yada shirye-shirye dake harzuka 'yan kabilar Igbo.
Sakamakon wannan zangazangar ce Shugaba Buhari ya aika da wata tawaga zuwa birnin Fatakwal din domin ganin halin da ake ciki.
Shugaban tawagar Alhaji A.D.C Barde yace sun gana da kwamishanan 'yan sandan jihar Rivers. Sun zauna dashi kuma ya nuna masa shaida akan abun da ya faru. An ji ma 'yan arewa wajen arba'in ciwo har wasu sun fara gudu daga birnin. Kawo yanzu 'yansanda sun kama mutane takwas kuma zasu kaisu kotu.
Alhaji Barde ya gana da sarakunan kabilun da su jawo hankalin matasan su kuma fada masu gaskiya. Yace zaman lafiya kasar ke nema ba tashin hankali ba.
Har yanzu dai al'ummar arewa dake Fatakwal suna zaman dar dar.
Ga karin bayani.