Rundunar Sojin Najeriya Ta Ce Ta Na Aiki Tukuru Da Dakarun Kasar Kamaru

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta na aiki tukuru da dakarun kasar Kamaru, kuma ba da dadewa ba za ta fara aiki da na Chadi domin kawo karshen rikicin Boko Haram.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta na aiki tukuru da dakarun kasar Kamaru, kuma ba da dadewa ba za ta fara aiki da na Chadi domin kawo karshen rikicin Boko Haram. Sabon babban hafsan sojin kasa na kasar, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ne ya sanar da hakan lokacin da ya ziyarci dakarun da ke yaki da Boko Haram a jihar Borno.