Rundunar sojin kasar Kamaru ta ce ta kashe mayakan ‘yan aware 24, da suka lashi takobin tarwatsa zaben da za a sake yi a yankunan kasar masu magana da harshen turanci.
To amma shaidun gani da ido sun ce mafi akasarin wadanda aka kashe, farar hula ne da aka same su suna fada da juna.
Kwamandan rundunar sojin Brigadiya Janar Valere Nka, ya bayyana cewa dakarunsa sun kai farmaki tare da tarwatsa sansanoni 10 na mayakan, a zaman wani yunkuri na samar da kyakkyawan yanayin gudanar da zaben da ake shirin yi ranar Lahadi.
Ya kuma ce dakaru 350 da aka tura a yankunan dake magana da turanci, sun kama motoci da makaman ‘yan awaren, a yayin da suka kashe mayakansu da dama, ciki har da kwamandansu.
A nasu bangaren, ‘yan awaren sun rubuta a kafar sada zumunta ta yanar gizo cewa sojoji sun lalata sansanoninsu, amma sun ce mafi akasarin wadanda suka mutu ko jikkata, daga bangaren sojojin suke..
To amma kuma Janar Nka ya ce, sojojinsa sun dawo da ransu su duka, sai dai ‘yan raunuka da wasu suka samu.