Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Soke Sallar Juma'a a Nijar


Wasu musulmai 'yan kasar Indiya yayin da suke sallah
Wasu musulmai 'yan kasar Indiya yayin da suke sallah

Bayan da hukumomin kiwon lafiyar al’umma a Jamhuriyar Nijar suka ba da sanarwar gano mutum na farko da ya kamu da cutar coronavirus, an soke sallar Juma'a a kasar.

An gano cewa mutumin mai shekara 36 yana dauke da cutar ne bayan da likitoci suka gudanar da bincike kansa, a lokacin da aka ga alamunta tare da shi yayin da aka tsayar da shi kan hanya.

Mutumin dai dan kasar ta Nijar ne wanda ke aiki a wani kamfanin zirga-zirga, kuma lokacin da aka gano yana sauke da cutar ya iso birnin Yamai ne bayan ya fitowa daga Burkina Faso.

Jim kadan bayan lamarin ne hukumar koli ta adinin musulunci ta soke sallarJuma'a da kuma sallar jam'i a duk fadin kasar.

An dauki wannan matakin ne domin kaucewa yaduwar wannan annoba kamar yadda ministan kiwon lafiya Dr iliassou Idi Mainassara ya sheda wa Muryar Amurka.

Hakan duk na faruwa kwanaki kadan bayan da kasar ta rufe kofofinta ga 'yan kasashen waJe domin takaita yaduwar cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG