Hanyar dai na daya daga cikin manya-manyan hanyoyin da rundunar sojan ta haramta bi, tun daga ranar 1 ga watan Satumbar 2014, sakamakon yakin da take yi da ‘yan kungiyar Boko Haram a yankin da ke kusa da dajin Sambisa.
An dai gudanar da bikin bude hanyar ne a yau Asabar, inda mataimakin gwamnan jihar Alhaji Usman Mamman Durkwa ya wakilci gwamnan jihar Kashim Shettima.
Da yake yi wa Muryar Amurka karin hasken kan bude hanyar, Alhaji Usman, ya ce bude hanyar zai kawo ci gaba ga al’ummar yankin tare da karfafa dangantaka da sauran makwabtan kasashe.
Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Majo Janar Rogers Nicholas, ya ce, bayan nazari da suka yi da tabbatar da cewa babu wata sauran barazana kan hanyar ya sa suka yanke shawarar sake bude ta.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5