Rundunar Sojan Najeriya Ta Maida Martani Ga Sanata Baba Kaka Bashir Garbi

NIGERIA BORNO BOKO HARAM IN BAMA

Hedkwatar tsaron Najeriya ta maida martani ga Sanata Baba Kaka Bashir Garbai kan kalamansa na cewa yan Boko Haram har yanzu suna rike da galibin sassan jihar Borno.

Cikin wata tattaunawar da yayi da Muryar Amurka, Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Borno ta tsakiya Sanata Baba Kaka Bashir Garbai, ya gwada cewa har yanzu yan Boko Haram ke rike da galibin sassan jihar Borno, inda yace “karamar hukuma uku ne babu yaran nan Maiduguri da Bayo da Kwaya Kusar, in banda wadannan kananan hukumomin, garuruwan da ke hannun hukuma cikin 100 ba zai wuce 30 ba.”

Amma cikin martanin da ta mayar Rundunar sojojin Najeriya, tace ko da yake bata son yin cacar baki da shugabannin siyasa, amma bata ji dadin kalaman Sanata Baba Kaka Bashir Garbai ba. inji daraktan watsa labarai na rundunar Birgediya Janaral Rabe Abubakar.

Wanda yace “A matsayin mu na sojoji bama son kawo wata magana tsakanin mu da shugabannin siyasa, ba sai mun fada ba su kansu yan Najeriya sun sani ai, yanzu muna ci gaba da rusa dukkan inda yan Boko Haram suke, muna amfani da sojojin sama da na kasa muna aikin da yakamata muyi……”

Kalaman na Sanata Garbai ya biyo bayan wani harin ba zata da yan Boko Haram suka kai Galori a jihar Borno, harin da har yanzu masu sharshi kan al’amuran tsaro ke mamaki. Amma Janaral Rabe Abubakar yace, irin wannan hari nan gaba ba zai sake faruwa ba.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojan Najeriya Ta Maida Martani Ga Sanata Baba Kaka Bashir Garbi - 2'00"