Ita dai kungiyar Amnesty International, na zargin rundunar sojan Najeriya da sake mayar da tsohon babban kwamandan runduna ta 7 na sojan Najeriya dake Maiduguri, Major Janal Ahmadu Mohammed bakin aiki, bayan da akayi masa ritayar dole a shekara ta 2014.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojan ta fitar, tace anyi wa Janal Mohammed ritayar dole ne ba bisa ka’ida ko la’akari da dokokin soji ba, abin ke nan da yasa bayan ya gabatar da kukansa a hukumance ga majalisar soja, aka duba a tsanake daga baya kuma aka sake mayar da shi bakin aiki.
Kakakin rundunar sojan Najeriya Kanal Kuka Sheka ya shaidawa wakilin Muryar Amurka Hassana Maina Kaina, cewa an dawo dashi baikin aiki, amma yadda kungiyar ta dauka ba haka abin yake ba, domin lokacin da aka sallameshi ba a bi ka’idar yadda yakamata ba.
Shi kuma kwararre kan aikin soja kuma tsohon gwamnan mulkin soja a jihohin Kano da Benue, Kanal Aminu Isa Kwantagora, yace kungiyar Amnesty International tayi gaggawar fitar da sanarwa akan wannan al’amari.
Your browser doesn’t support HTML5