Daukar matakin sallamar ya biyo bayan wani bincike da rundunar sojan Najeriya ta gudanar, game da rawar da sojoji suka taka a zaben da akayi a jihohin Osun da Ekiti da kuma zaben shugaban kasa a aka gudanar a shekarar da ta gabata.
Haka kuma rahotanni sun bayyana cewa akwai wasu sojoji guda 12 da yanzu haka aka mika su ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC, domin gudanar da binciken zarginsu da akeyi na karbar na Goro daga hannun wasu manyan yan siyasa kasar a wancan zaben da aka gudanar.
Daga cikin sojojin akwai Majo Janal guda 3 da kuma wasu Burgediya Janal guda 3 da hafsoshi masu mukamin Kanal guda 4 da kuma Laftanal Kanal guda 1.
Kakakin rudunar sojan Najeriya, kanal Sani Usman Kuka Sheka, shine ya tabbatar da daukan wannan mataki akan hafsoshin sojan, ya kuma ce an tura Kaftin Sagir Koli jami’in asirin sojin nan da ya fallasa wannan abin kunya a wancan lokaci, domin karo karatu a wata kasa ta katare.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5