Rahottani daga Iraq na cewa mayakan adawa na IS yanzu sun dawo suna dogaro akan yankunan dake hannunsu a kasar Syria su aiko musu abinci da sauran kayan aiki a inda suke cikin Iraq, inda kasashen duniya ke bada tallafi don a kwace muhimmin birnin nan na Mosul.
WASHINGTON, DC —
Jaridar “Smart News” da ake bugawa a can Syria tace an ga manyan motocin daukan kaya kamar 15 shake da kayan Miya, Sukari, Filawa, Shinkafa da sauransu sun tasarwa Mosul daga Raqqa.
A yanzu dai ance rundunonin mayaka sunyi wa garin na Mosul kawanya daga bangarori ukku, koda yake sum a mayakan na IS har yanzu, in suna so, suna da mafitar da zasu bi, ta yammacin garin, su fada cikin wata Hamadar da zata kaisu Syria, yankin da akace saboda girmansa sojan Iraq da Kurdawa ba zasu iya sarrafa shi ba.