Mayakan Sojin Saman Najeriya dake fafatawa a rundunar Operation Lafiya DOLE Mai yaki da Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya, ta rugurguza wani sansanin da mayakan Boko Haram ke Horas da mayakansu a zirin yankin tafkin chadi, bayan da jiragen yakinta sukai ta ruwan boma bomai ba ji ba gani..
A cikin wata sanarwar da kakakin hedkwatar sojojin saman Najeriya Air Commodore Ibikunle Daramola ya aikewa manema labarai, ya yi bayanin cewa jiragen yakin rundunar sunyi ta ruwan wuta a sansanonin boko haram dake zannari da Tumbin Rago dake yankin tafkin chadi bayan da aka sami sahihan bayanan sirri cewa lalle mayakan Boko haram sun kakkafa sansanonin samar da horo a yankunan
Take aka tayar da jiragen Yaki samfirin Alpha Jet,inda ya afkawa sansanonin ya yi ta masu ruwan wuta ba kakkautawa, daga bisani dai jirgin yakin ya hango wasu yan tsirarun mayakan na Boko Haram na kokarin arcewa inda nanma jirgin ya bisu kuma ya karkashe.
hedkwatar sojojin saman Najeriyar tace jami"ai da jiragen soji masu tattara bayanan sirri zasuci gaba da aiki wurjajan a shiyyar arewa maso gabas da ma zirin yankin tafkin chadin har sai an kammala gano maboya da dan abin da ya rage na sansanonin yan ta"addan Boko Haram din kuma a gama dasu.