Rukunin Karshe Na Dakarun Jamus Ya Fice Daga Nijar

Wasu Dakarun Jamus

Rukunin karshe na dakarun Jamus wanda adadinsa ya kai 120 ya kammala ficewa da kayansa daga Nijar kamar yadda Jamus ta cimma yarjejeniya da hukumomoin mulkin sojojin kasar da suka bukaci su fice kamar yadda ta kasance da sojojin Faransa da na Amurka.

Kafin tashin jirgin sojojin na Jamus rudunonin sojojin kasashen biyu dai sun fitar da sanarwar hadin gwiwa ta tabbatar a hukumance da kawo karshen kammala kwashe sojojin na Jamus daga Nijar tare da rufe sansanonin su daga kasar wanda aka soma tin a watan Agustan da ta gabata.

Masu sharhi kan al’amurran tsaro irin su Mohamed dilla na ganin akwai bukatar gwamnatin Nijar ta sake nazari game da ficewar sojojin Jamus ganin irin gudunmawar da suke bai wa kasar domin magance matsalolin tsaro da suka addabi jama'a.

Duk kuma da cewa ba’a samu sakamako mai ma’ana ba bayan shekaru fiye da takwas kasancewar sojojin kasa da kasa amma salon mulkin gwamnatin soji da Abourahamane Tchaini ke jagoranta bai kawo sauki a hulda da kasashen yamma irin Jamus ba.

Sai dai tuni kungiyoyin fafutuka na Nijar suka bayyana jin dadin su da ficewar sojojin na Jamus daga kasar.

Duk da ficewar dakarun na Jamus dai wasu kungiyoyin farar fulla a Nijar ba su yanke kauna ba da sake sabuwar alakanta tsaro tsakanin kasashen biyu ba.

Sojojin na Jamus sun barwa Nijar wasu daga cikin kayayyaki da suka hada da motoci da na’urori da rumfuna da sauran su.

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:

Your browser doesn’t support HTML5

Rukunin Karshe Na Dakarun Jamus Sun Gama Ficewa Da Kayansu Daga Nijar