Rufe Hanyoyin Sadarwa Da Gwamnati Ta Yi Ya Sa 'Yan-Bindiga Kara Farashi Kudin Fansa - Shugaban CAN

'Yan Bindiga

Ganin yadda 'yan-bindiga ke cigaba da afkawa garuruwa da kuma sace mutane don neman kudin fansa duk da matakan da gwamnonin Arewa maso yamman su ka dauka ya sa wasu kiran sauya salo.

Sama da wata guda ke nan da gwamnatin jahar Kaduna ta bi sahun sauran takwarorin ta na Arewa maso yamma don rufe hanyoyin sadarwa da wasu matakai sai dai kuma kungiyar Kiristoci ta kasa CAN ta ce kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

Shugaban kungiyar ta CAN, reshen jahar Kaduna, Rabaren John Joseph Hayeph ya ce rufe hanyoyin sadarwa da gwamnatin jahar Kaduna ta yi ya sa yanzu 'yan-bindiga sun kara farashi kudin fansa.

Shi kuwa mai nazari akan al'amuran yau da kullun, Malam Abubakar Aliyu cewa ya ke rashin tuntubar mutane kafin daukar matakan tsaro ke kawo koma baya.

Sai dai gwamnatin jahar Kaduna ta ce masu saka siyasa ne ke sukar wadannan matakan tsaro na bai daya, inji kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Malam Samuel Aruwan.

Ko a ranar Lahadin da ta gabata dai sai da 'yan-bindiga su ka kai hari wata cocin Baptist da ke Kakau daji, kamar dai yadda shugaban kungiyar Kiristoci na jahar Rabaren John Joseph Hayeph ya tabbatarwa da Muryar Amurka.

Rufe hanyoyin sadarwa da hana hawa babura da gwamnatin jahar Kaduna ta sanar dai na watanni uku ne a karon farko kuma sai yanzu aka yi wata guda da farawa, wanda wannan ne ke kara kawo fargaba na sauran lokachin da ke gaba.

Saurare cikakken rahoton a cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Rufe Hanyoyin Sadarwa Da Gwamnatin Kaduna Ta Yi Ya Sa 'Yan-Bindiga Su Kara Farashi Kudin Fansa - Shugaban CAN