Shugaban Iran, Hassan Rouhani, ya gaya wa Shugabannin kasashen duniya jiya Laraba cewa, kasar Iran ba za ta yi zaman tattaunawa da Amurka ba, muddun takunkumin da aka kakaba ma ita Iran din na aiki.
“An taba yin zaman tattaunawa da mu alhalin takunkumi na aiki a kanmu. Ba za mu sake yadda da haka ba. A tsai da takunkumin sannan a koma kan alkawuran da aka yi, watakila a iya sake bude babin tattaunwa,” abin da Rouhani ya gaya ma Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya kenan.
Amurka ta kakaba takunkumi kan wasu muhimman bangarori na sashin man kasar Iran, bayan janyewar da Amurkar ta yi bara daga yarjajjeniyar da aka cimma a 2015, wadda ta tanaji takaita shirin nukiliyar kasar Iran.
Gwamnatin Trump ta ce yarjajjeniyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya ba ta yi tasiri ba sosai, wajen hana Iran ci gaba da shirinta na makaman nukiliya da kuma yin wasu aika-aika.