Ronaldo: Portugal ta kammala shirye-shirye don fafatawa da Belgium

Your browser doesn’t support HTML5

Ronaldo: Portugal ta yi atisaye a filin wasa na La Cartuja da ke Seville ranar Asabar - sa’o’i 24 kafin su kara da Belgium a wasan zagaye na 16 na Euro 2020.
Portugal ta yi atisaye a filin wasa na La Cartuja da ke Seville ranar Asabar - sa’o’i 24 kafin su kara da Belgium a wasan zagaye na 16 na Euro 2020. Cristiano Ronaldo tare da sauran suna fuskantar jarrabawa mai tsauri akan kungiyar da take matsayi na daya a duniya wacce ta lashe duka wasanninnsu uku. Portugal na burin samun nasarar lashe gasar cin kofin Turai karo na uku a jere, bayan da ta ci Euro 2016 da kuma nasarar lashe gasar League Nations a shekarar 2019.

Karin bayani akan: UEFA EURO 2020, Cristiano Ronaldo, Portugal, da Belgium.