Ronaldinho Zai Auri Mata Biyu A Lokaci Guda

Tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa daga Brazil Ronaldinho, zai auri ‘yan matansa biyu duk a lokaci guda, kamar yadda mujallar The Mirror, ta bayyana.

Za a daura auren ne tsakanin Ronaldinho da Priscilla Coelho da kuma Beatriz Souza a cikin watan Agustan wannan shekarar.

A cikin watan Janairun shekarar da ta gabata ne dan wasan ya mikawa ‘yan matan biyu zoben bukatar neman amincewarsu da aure.

Matan biyu na zaman lafiya da juna da kwanciyar hankali tare da tsohon dan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona tun watan Disambar shekarar da ta gabata a makeken gidansa da ke Rio de Janeiro wanda aka kiyasta kudinsa zai kai Fam miliyan biyar.

Ronaldinho ya fara neman Beatriz a shekarar 2016, amma ya ci gaba da nema da Priscilla, wadda ya dade yana nema.

Rahotanni sun bayyana cewa duka ‘yan matan nasa suna karbar kudaden alawus na kusan Fam 1,500 na kashewa daga wurin tsohon dan wasan.

‘Yar uwar tsohon tauraron dan wasan wadda ba ta yarda da auren fiye da mata guda ba, ta ce ba za ta halarci daurin auren ba.