Rokokin Da Rundunar Sojin Amurka Ke Girkewa Za Su Iya Cafke Makaman Koriya

Rundunar sojan Amurka tace wani jerin makaman kakkabo rokokin da take girkewa a Koriya ta Kudu zai iya cafko duk wasu makamai masu linzami da Koriya ta Arewa zata iya cillowa.

Sai dai duk da wannan karfin imanin da suka nuna akan igancin wannan garkuwar da suke kira THAAD, rundunar sojan Amurka, ta ce har yanzu yana bukatar a dada yi mishi kwaskwarima kafin a soma cin moriyar sa.

Ana dai kafa wannan garkuwar ne a wani filin wasan golf dake Seongju da zimmar yin anfani da shi wajen kare Koriya ta kudu daga hare-haren Koriya ta Arewa.

Sai dai kuma China ta bayyana adawa da kafa wannan garkuwar ta THAAD, abinda take gani kamar barazana gare ta, ita kanta.

Dangane da hakan ne, a jiya kakakin ma’aikatar harakokin wajen China, Geng Shuang, yake gaya wa manema labarai cewa China, ta nemi a cire garkuwar ba da bata lokaci ba.