Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-zangar Ranar Ma'aikata a Fadin Duniya


Maus Zanga-zangar Ma'aikata na Duniya
Maus Zanga-zangar Ma'aikata na Duniya

Masu zanga zanga a nan Amurka da wasu sassa na duniya sun yi bikin ranar ma’aikatan ta duniya tare da gudanar da taruka da yin zanga zanga da ya kai ga tashin hankali na nuna fushi da kyamar mulkin kama karya da kuma siyasar gurguzi daga Faransa da kuma Turkiya.

Ranar ma’aikatan ko kuma May Day rana ce da aka saba gudanar da zanga zanga kamar ta wannan shekara. Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a kan masu zanga zanga dake gudanar da taro a Taksim Square a Istanbul, wurin da aka zubda jinni a wadansu tarukar ranar ma’aikatar a baya.


Tashin hankali a Turkiya ya kara ta’azzara biyo bayan wani karamin rinjayi da shugaba Racep Tayyib Erdogan ya samu a zaben raba gardama a watanr da ya gabata inda shugaban ya lashe wasu madafun ikon kasar.


A jiya Litinin yan sanda sun kama mutane sama da 200.


A kasar Venezuela kuma zanga zangar ma’aikatar ya zama tashin hankali inda aka samu masu ra’ayi da kuma masu kin jinin gwamnati suna gudanar da zanga zanga. Jami’an tsaro a babban birnin kasar Caracas,sun yi amfani da barkonon tsohuwa a kan matasar dake jifansu da duwatsu da suke zanga zangar kin jinin gwamnatin gurguzu ta shugaba Nicholas Maduro.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG