Wasu majiyoyi na cewa kawo yanzu fiye da mutane talatin ne suka rasa rayukansu tare da jikkata wasu fiye da hamsin.
Mr Bako Benjamin Dan Borno shugaban hadakar cigaban jukunawa yace mutum talatin da uku ne aka kashe, wadanda kuma suka ji ciwo hamsin da uku. Inji Bako, yace yayinda yake magana da wakilin Muryar Amurka mata da yara sun fito suna zanga-zanga akan basa son abun dake faruwa. Yace mutun nan zaune a kofar gidansa sojoji zasu bude masa wuta.
Dangane da ko shugabannin sun yi wani kokarin kawo zaman lafiya, Bako yace shin sau nawa zasu zauna su yi sulhu. Sun yi zaman sulhu wajen guda shida kowane kuma suna cimma yarjejeniya. Yace sun zauna sun yi sulhu. Jukunawa musulmi da kirista suke fada da juna. Yace shin me ya kawo hakan. Me yasa ba zasu yi hakuri da juna ba. Me yasa ba zasu yafewa juna ba.
Akwai kuma rahoton dake cewa wasu mahara suna tare hanya suna farma matafitya. Wani ganao yace maharan sun rufe hanya a jeji duk motocin dake zuwa Adamawa, Maiduguri sun hanasu wucewa. Yace yakamata gwamnati ta dauki mataki akansu.
Sun sha zaman sulhu amma abun mamaki 'yan kwanaki kadan bayan an yi sulhu sai wani rikici ya sake kunno kai. Rikicin baya bayan nan an yi zaman lafiya da kwana huhu ya barke. Sarkin Donga shi ya hada taron amma ana gamawa sai wannan rikicin ya tashi . Jukunawa da ba musulmai ba suna kiran jukunawa musulmai hausawa. Mai magana yace su sani cewa son juna shi zai kawo zaman lafiya.
Hukumomin tsaron jihar suna cewa kullum suna kokarin shawo kan lamarin su kawo zaman lafiya. ASP Joseph Kwaji kakakin rundunar 'yansandan jihar yace sun hada gwiwa da sojoji suna sintiri a garin Wukarin. An kafa dokar hana fita domin kada wani abu ya sake faruwa. 'Yansandan jihar sun sake cewa mutum shida suka mutu a rikicin.
Karo na shida ke nan da aka samu rikici a garin Wukari. Rikicin yakan komawa na kabilanci da addini. Mr. Kefas Sule jami'in yada labarai na mukaddashin gwamnan jihar yace gwamnati zata dauki mataki mai tsanani akan duk wadanda ke da hannu a rikicin yadda babu wanda zai sake tada rikici nan gaba.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5