Rikicin Siyasa a Jam'iyyar NNPP Yayi Sanadiyyar Dakatar Da Kwankwaso

Dr. Rabiu Kwankwaso

Jam’iyyar People’s Nigeria (NNPP) ta shiga cikin wani rikici na cikin gida da ta kai ga dakatar da wasu manyan jam’iyyar da suka hada da fitaccen dan siyasa Rabiu Musa Kwankwaso.

A wani taro na musamman da aka gudanar a otal din Rockview dake Apapa a Legas, wasu ‘yan jam’iyyar NNPP da suka bayyana kansu a matsayin kwamitin amintattu sun kada kuri’ar dakatar da tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya zo na hudu a zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Rahotanni sun bayyana cewa wata kungiya ce a karkashin jagorancin Mista Boniface Aniebonam da Agbo Major wasu kusoshi a jam’iyyar ta NNPP, ta bayyana matakin dakatar da Kwankwaso bayan taron da ta gudana a Jihar Legas. Haka zalika sun sanar da dakatar da kwamitin zartarwar NNPP na kasa.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, kungiyar na zargin Kwankwaso da hanu dumu-dumi cikin abinda ya shafi yiwa jam’iyya zagon kasa, musamman la’akari da taruka daban daban da ya halarta tare da 'yan adawa alal misali, taron Kwankwaso da shugaba Tinubu, da kuma wanda yayi da tsohon dan takarar shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar wanda yazo na biyu a zaben 2023, da kuma Peter Obi da yazo na uku.

A cewar su, matakin yazo ne bayan wani bincike da kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar ya gudanar bisa zargin da ake wa Kwankwaso.

Har ila yau, kwamitin na amintattun na Boniface Aniebonam yayi sabbin nade-naden shugabannin NNPP na kasa, inda Dr. Agbo Major ya zama shugaban jam'iyyar na riko, sai Kwamared Ogini Olaposi, matsayin sakataren NNPP na ƙasa da kuma sauran jami'ai 18.

A wata sanarwa da suka fitar bayan kammala taron na Legas, an ambaci cewa Boniface Aniebonam ya sauka daga matsayin shugaban kwamitin amintattu, kuma nan take taron ya zabi Tope Aluko matsayin wanda zai maye gurbin sa, sannan da Babayo Abdullahi a matsayin sakataren kwamitin amintattun.

A bangaren sa Kwankwaso, magoya bayansa sun ce mutanen da suka aiwatar da wannnan dakatarwa haramtattu ne, domin tuni an rigada an kore su a jam’iyyar tuntuni.

Suna masu cewa jam’iyyar NNPP tana fuskantar matsin lamba daga waje, kuma wasu mutane na yunkurin kawo rudani da nufin rugujewar jam’iyyar ne domin cimma burinsu.

An gudanar da wani taro makamancin wannan da ake kira taron kwamitin zartaswa na kasa (NEC) a Abuja, inda jiga-jigan jam’iyyar da suka hada da Malam Buba Galadima, shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, da wasu kusoshi a jam’iyyar, suka kira domin tattauna rikicin da ke faruwa. A yayin wannan taron, an bayyana cewa an dakatar da Aniebonam da Boniface Major daga jam’iyyar.

Haka zalika, taron na Abuja ya gabatar da wasu sabbin kudurori da suka hada da gyaran tsarin mulkin jam’iyya, batun tambarin jam’iyyar, tabbatar da kwamitocin riƙon ƙwarya na jihohi da sauransu.

Wanan rikici da ya kunno kai a jam’iyyar NNPP ya sanya ayar tambaya kan makomar jam’iyyar da kuma yanayin siyasar Najeriya. Wasu masu lura da al’amura dai na hasashen cewa wannan rikici na cikin gida na iya alakanta shi da manyan kawance da fafatawa a siyasance, inda zabukan 2027 ke kara kusantowa.

A yayin da jam’iyyar NNPP ke fama da rarrabuwar kawuna a cikin gida da rigingimun madafun iko, har yanzu babu tabbas kan yadda jam’iyyar za ta ci gaba da tafiyar da harkokinta a siyasar Najeriya. Makwanni masu zuwa na iya zama muhimmai wajen tantance hanyoyin da jam’iyyar za ta bi da kuma rawar da za ta taka wajen tsara makomar ta a siyasar Najeriya.

~ Yusuf Aminu Yusuf ~