Shugaban Najeria Muhammadu Buhari ya ce, rikicin shugabanci da kasar Libya ta tsinci kanta a ciki, na taka muhimmiyar rawa wajen karuwar matsalolin tsaro da ke addabar kasashen yankin Tafkin Chadi da na Sahel.
Kalaman Buhari na zuwa ne yayin da shugabannin kasashen yankin suke wani taro na musamman a Abuja, babban birnin Najeriya, don duba yadda za a marawa kasar Chadi baya, wajen ganin ta koma kan turbar dimokradiyya.
“Rikicin Libya ya kara jefa kasashen yankin Tafkin Chadi da na Sahel cikin matsalolin tsaro, saboda yawaitar makamai, harsashai, miyagun kwayoyi da kwararar ‘yan gudun hijira da ake ci gaba da samu, wadanda duk suke barazana ga tsaron yankin.” Buhari ya fada yayin bude taron, kamar yadda wata sanarwa da kakkinsa Femi Adesina ya fitar ta ce.
Libya ta fada cikin rikicin siyasa, bayan hambarar da gwamnatin Moammar Ghaddafi a shekarar 2011, tun daga lokacin, kungiyoyi masu dauke da makamai ke ta ja-in-ja kan shugabancin kasar.
Kasashen da ke halartar taron na kwana daya a Abuja, sun hada da Nijar, Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, Chadi, Kamaru, Libya da kuma Sudan.
Buhari wanda shi ke jagorantar kungiyar kasashen, ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen da ke yankin Tafkin Chadi su hada kansu su yi aiki tare, domin tunkarar matsalolin da suka yi wa yankin katutu.
“Yankinmu na fuskantar wahalhalu, akwai kalubale da dama da ke bukatar hadin kan kowa da kowa don a shawo kansu.”
Dangane da abin da ya hada taron, shugaban na Najeriya ya ce, akwai bukatar mambobin kungiyar su marawa Chadi baya don ganin ta magance matsalolinta na cikin gida.
“Ya zama dole mu dauki barazanar da kungyoyin ‘yan tawayen Chadi ke yi na kifar da gwamnatin kasar da muhimmanci, saboda abin da zai biyo baya idan Chadi ta shiga matsala ba zai misaltu ba.”
A watan Afrilu shugaban Chadi Idriss Deby Itno ya rasu bayan raunuka da ya samu a fagen yaki a cewar dakarun kasar.
Daga baya an nada dansa Janar Mahamat Idriss Deby a matsayin shugaban kwamitin soji na rikon kwarya.
Najeriya na fama da matsalar mayakan Boko Haram da ISWAP da masu garkuwa da mutane, yayin da Nijar da ke makwabtaka da ita, ke fama da matsalar ‘yan bindiga daga Mali.
Kamaru kuwa na fama da matsalar ‘yan aware da ke so su bangaren daga arewacin kasar yayin da ita ma Jamhuriyar tsakiyar Afirka ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.