Rikicin Kano Zai Iya Shafar Masarautun Arewa - Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya yi gargadin cewa, rikicin kirkirar sabbin masarautu a jihar Kano, zai iya shafar sauran masarautun da ke yankin arewacin Najeriya.

"Maganar a yi masarautu a Kano ba ta ko taso ba, in dai ana haka, sarauta za ta lalace a arewa." Inji Bafarawa.

Bafarawa ya yi wadannan kalamai ne, yayin wata ziyara da ya kai ofishin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Washington.

Ya kara da cewa, tuntuni, shugaba Muhammadu Buhari ya kamata ya sa baki a wannan magana a "matsayinsa na shugaban kasa kuma dan arewa," yana mai cewa, shi kadai ne zai iya shawo kan lamarin.

An dai kwashe watanni da dama ana takun saka, tsakanin masarautar Kanon da gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Lamarin ya kai ga Ganduje ya kirkiri wasu sabbin masarautu hudu, matakin da wasu ke ganin martani ne ga Sarki Muhammadu Sanusi II, wanda ake zargin yana yawan sukar lamirin gwamnatin jihar.

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar ta Sokoto, wanda ya ce maganar da ya yi ta "ra'ayinsa ne na kansa," ya kara da cewa, "tun da ma ban goyi bayan raba Kano ba."

"Bai kamata a zo ana wasa ana sa siyasa a masarauta irin ta Kano ba."

Saurari hirarsu cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Rikicin Kano Zai Iya Shafar Masarautun Arewa - Bafarawa