An yi tashin hankalin da ya yi sanadiyar jikata mutane 20 tare da kona kasuwa da kaddarori a garin Gulu cikin jihar Neja. Shaguna da dama aka kone a cikin garin.
Bayyanai sun tabbatar da cewa rikicin iyaka ne ya kawo tashin hankalin tsakanin Gulu ta arewa da kuma Gulu ta yamma.
Alhaji Muhammed Sani dagacin garin Gulu ta arewa yayi karin haske akan asarar da aka samu lokacin tashin hankalin. Yace kodayake ba'a yi asarar rai ba amma wadanda suka jikata zasu kai ashirin ko talatin. An kone shaguna da gidaje da dama.
Tuni mahukuntan jihar Neja suka ce sun dauki matakan shawo kan matsalar kamar yadda Dr. Isa Yahaya Batsa kwamishanan ma'akatar dake kula da harkokin dabbobi wanda kuma ya fito daga yankin yace. Inji shi ana nan ana yin taro domin a lalubo bakin zaren warware matsalar.
Rundunar 'yansandan jihar ita ma ta tabbatar da aukuwar rikicin. Tace ta tura karin jami'an tsaro a yankin domin dawo da doka da oda.
Ga rahoton Mutapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5