Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Dake Maiduguri ta Tsawaita Zirga-zirgan Ababen Hawa


Manjo Janaral Chris Olu Kolade kakakin rundunar sojin Najeriya.
Manjo Janaral Chris Olu Kolade kakakin rundunar sojin Najeriya.

A birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno rundunar soji ta tsawaita zirga zirgan ababen hawa sabili da dalilan tsaro.

Tsawaitawar zata far aiki ne daga yau Litinin har zuwa gobe Talata da karfe bakwai na safiya.

Mataimakin daraktan hulda da jama'a na sojojin Kanal Sani Usman shi ya aika sanarwar ga manema labarai. A cikin sanarwar yace rundunar ta kara kwana guda bisa ga wa'adin da aka bayar tun can farko. Yanzu sai gobe Talata da safe za'a cigaba da zirga-zirga kamar yadda aka saba.

Tun ranar jajiberen sallah rundunar ta fitar da sanarwa inda ta haramta zirga-zirga a fadin jihar baki daya sabili da wai sun samu rahoto dake cewa wasu mahara suna shirin kai hare-hare a filayen idi da kasuwanni.

Bayan cika kwanaki biyu da hana zirga-zirgar sai rundunar ta sake fitar da wata sanarwar karin kwana daya.

Yanzu dai al'ummomin Borno da Yobe suna cigaba da bukukuwan salla a wuraren da aka kebe sakamakon haramta ababen hawa da aka yi masu da kuma kulle jihar Borno gabaki daya. Wasu na ganin hakan ba zai rasa nasaba da irin matakan tsaron da sojojin ke dauka ba domin hana mahara aiwatar da yadda suke so.

To sai dai tsawaitar zirga zirgan bai shafi ma'aikatan kwana-kwana ba da kuma jam'an tsaro dake yin sintiri.

Sanarwar karin kwana guda ta zo wa alummar jihar Borno bazata. domin mafi yawan jama'a sun shirya ne domin gudanar da harkokinsu irin na yau da kullum yau Litiinin.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG