Al’amarin dai ya tilastawa mata da yara kimanin dubu biyar kauracewa gidajen su.
Tun da marecen ranar lahadin da ta gabata ne al’umar garuruwan Gayin babba, Gayin karama, Mattafari, Banjari, Dandori, Dolen Dandori, Kukadabu, Gangabituwa ke cikin yanayin zaman dar-dar sakamakon wannan fitina.
Alhaji Mohammed Mohammed Adamu dake zaman Bulaman garin Zangayan wanda Bafulatani ne ya yi karin haske inda ya ce dukkan bangarorin a sami rauni, yanzu haka dai kokari ake yi a ga an hada karfi da karfe don a ga yadda za'a sasanta lamarin.
Karin bayani akan: Fulani, Nigeria, da Najeriya.
Yanzu haka dai mutane kimanin dubu biyar ne, musamman mata da yara suka tsere zuwa manyan garuruwa irin su Birniwa da Hadejia da kuma Ngurunjihar Yobe saboda gudun abin da ka je ya zo, a cewar Malam Mohammed Hassan wani mazaunnin garin Gayin Babba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Usman Gomna ya ce tuni dai hukumomin tsaro a jihar ta Jigawa suka dauki matakan dakile wannan fitina.
Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce dangane da matakin gwamnonin kudancin Najeriya na hana Fulani kiwo a dazukan da ke yankunan su, har-ma gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi tayin Filin kiwo ga Fulani ‘yan asalin jihar sa da aka koro daga Kudu.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5