Rikicin Cikin Gidan APC Yana Dada Haifar Da Rarrabuwar Kawuna

Nigeria National Assembly

Yayin da Gwamna Akeredolu ya ki amincewa da tsarin da APC ta fitar na shugabancin majalisa ta 10, Betara ya ce babu gudu ba ja da baya game da takarar shi na neman shugabancin majalisar sannan gamayyar hadin kan ‘yan arewa a majalisar ta ki amincewa da zaben Apkabio da Abbas.

Wannan al’amari yana nuna cewa gibin da ya bayyana a jam’iyyar yana dada fadada gabanin kaddamar da majalisar tarayyar ta 10 a watan Yuni mai zuwa, Akeredolu ya bayyana matakin kwamitin da karkatacce wanda zai dada karfafa rashin adalci da daidaito, ya kuma jaddada cewa mutanen da suke kewaye da zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ne suka dauki kansu tamkar kabal a dalilin kusancinsu da Tinubu duk laifinsa ne.

A ranar Litinin ne APC ta bayyana wadanda take ganin su suka fi dacewa da shugabancin majalisar inda ta tsara shugagabn majalisar dattawa ya kasance daga yankinkudu maso kudukuma suke ganin ya dace da Sanata Godswill Akpabio ayyyaa matsayin wanda ya dace sannan shi kuma Abbas Tajudeen ya zama kakakin majalisar Tarayya.

taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade

A wata sanarwa mai dauke da sa hannum,shi, wanda sakataren yada labaran shi Richard Olatunde ya raba, Akeredolu ya jaddada cewa tsarin karba-karban zai haifar da yanayin da zai yi wa jam’iyyar illa idan ba a gyara kuskuren da ya ce an yi ba. Ya kuma dage akan cewaya kamata a baiwa Arewa damar fada a ji a lamarin zaben wadanda zasu cike gurbin shugabancin majalisar musamman ma na kakakin majalisar wakilai, kana yayi sukar shugabannin jam’iyyar da suka ki baiwa gwamnonin jam’iyyar damar fadin ra’ayinsu akan wannan al’amari.