A Sudan ta kudu Kwanaki kadan bayan sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka sake farfado da ita, rahotanni sun nuna cewa fadace fadace sun barke a wadansu sassan kasar, a cewar Jean Pierre Lacroix, wakilin babban sakataren MDD na musamman kan ayyukan kiyaye zaman lafiya.
Lacroix ya shaidawa wakilan kwamitin sulhu na MDD a birnin NewYork cewa "rahotanni sun nuna cewa rikici ya barke ne ne bayan da gwamnati tayi kokarin kafa shugabannin kananan hukumomi a yankunan da suke hanun 'yan tawaye. Ya kara da cewa duka sassan biyu sun turo karin dakaru zuwa yankunan a matakin kama iko.
Ya kara da cewa rikicin na faruwa ne a jihohin Central Equatoria da Unity kana kuma an samu rikici sosai a cibiyar Jamula dake Mbudu a yankin Kopera.
A halinda ake ciki kuma wani rahoto da kungiyar kare hakkin Bil'Adama ta kasa da kasa Amnesty International ta fitar jiya Laraba, ta zargi sojojin gwamnti da laifin kona yara da tsoffi da ransu. An kuma yiwa mata giwa ta fadi. Tareda harbe farar hula har lahira, da bi ta kansu da motocin yaki masu sulke, ko a rataye su kan bishiyoyi ko jinka.