Masana harkokin tsaro na cewa, kara dagulewar yanayin tsaro a yankin arewa maso gabashin Nigeria ba ya rasa nasaba da sakaci daga bangaren jami’an tsaro, kamar yadda wani mai sharhi kan lamuran tsaro a Nigeria, Manjo Hassan Abdul’aziz mai ritaya ya fadi.
Yace shigar ‘yan Boko Haram sannanin ‘yan gudun hijira dake Rann abun mamaki ne, domin ya kamata sansanin na da tsaro fiye da tsammani da zai hana kowane irin hari da za’a kawo. Amma ‘yan ta’addan sun shiga sansanin har suka sace mutane da yanzu wata shida ke nan suna rike dasu. Gwamnatin Nigeria da Majalisar Dinkin Duniya, MDD, da suke yiwa aiki ba su yi komi ba har yanzu ‘yan ta’addan sun soma kashesu.
Mano Hassan Abdulaziz ya ce ba cin kasa ba ne abu riketa shi yake da mahimmanci. Sojojin Nigeria na ikirarin murkushe ‘yan Boko Haram amma bas u rike wuraren da suka kama daga ‘yan ta’addan. Bayan a tarwatsasu suna dawowa su sake haduwa su ci gaba da kai hare hare domin sub a sojojin Nigeria kunya.
Manjo Hassan ya ce sakacin sojojin ya say an Boko Haram kutsawa sansanin. Kamata ya yi ko kuda ne zai shiga wurin sojoji su kare saboda a lokacin wurin ya kunshi mutane fiye da 150,000.
Yace yankin arewa maso gabas ya koma gidan jiya saboda sojoji ba su yi abun da ya kamata su yi ba. Da sun ci gaba da kai masu samame, su hanasu sakat da ba su iya sake taruwa wuri guda ba. Baicin hakan duk wata hanya da aka sani suna samun kaya da sai a toshe, su kuma lura da baragurbi da ana iya samu ko a cikin sojojin ko kuma sojojin hadaka ko cikin fararen hula ma.
A saurari hirar da Manjo Hassan ya yi da Mahmud Kwari
Facebook Forum